Defamation of Character and Detention!!!
_______________________________
A doka irin ta Nigeria Aminu ya aikata laifin da Lauyoyi suke kira da "Defamation of Character", idan elements din da ake zargin sa sun tabbata, Kuma yana da hukuncin daurin shekaru uku a gidan Yari ko Tarar Naira Miliyan 7,000,000 a karkashin dokar da gwamnatin Nigeria ta amince da ita ranar 15 May 2015 na "Cyber Crime Protection Law" that's Online Crime.
~ Ita Kuma Mama ta Sabawa kundin tsarin mulkin Nigeria Section 35 da yace baya halatta a tsare wani mutum sama da Awanni 48 (kwana biyu), idan kuwa za'a tsare shi toh dole sai in Kotu ce tace aje a tsare shi.
(Right to Pre Trial Release), Section 35 (4) CFRN.
~ On trial Kuma babu Wanda aka yarda a tsare shi for more than four years ana Shari'a.
~ Idan muka koma CC, wato Criminal Code na Nigeria (Southern Part) zamu ga cewa Section 375 yace Wanda aka same shi da laifin Defamation of Character za'a hukunta ta hanyar daurin shekara daya a gidan Yari da sauran su na Tara ko dauri a hade da Tarar.
~ Idan muka koma Islamic Law zamu ga cewa irin wannan laifi idan har Kotu ta tabbatar da laifin sa za'a hukunta da Bulala 80.
~ Qazafi ko yarfe yana daga cikin abubuwan da Manzon Allah ya kausasa harshe wajen Jan kunnen Musulmi akai, misali:
~ Wata rana Nana Aisha (A.R) ta Kalli Safiyyah sai tace da ita (Gajeruwa kawai, Guntuwa, wada, me Manzon Allah ya gani ma har ya aure ki?).
Manzon Allah yace wa Nana Aisha (Kin Fadi maganar da in da za'a zuba ta a cikin ruwan Kogin Bahar Maliya sai ta lalata ruwan ta yadda ba za'a iya Sha ba), saboda girman wannan kalmar da kika fada.
~ Lokacin da Sayyidina Umar yace wa Hadib Ibni Abi Bal'ta'a makaryaci, Manzon Allah ya tsawatar masa cewa wannan maganar zata iya kawo fushin Allah.
~ Lokacin da Abu Zharr yace wa Bilal (Baki 'dan bakar mace) Manzon Allah yace (Kai Abu Zharr akwai dabi'un mutanen zamanin jahiliyya a tare da kai)...
Wadannan duk suna nuna munin kazafi, ka fadi abinda baka da ilimi akai ko kuma ka munana wa wani mutum.
~ Duk wadanda suka yada labarin Qazafin da aka yi wa Nana Aisha cewa wai tayi Zina (Allah ya tsare) sai da aka kamo su aka musu Bulala 80-80 aka hukunta su.
~ An hukunta su ne ba don sun taba matar Manzon Allah, No. Sai don sunyi laifi, Kuma hukuncin kenan a Musulunci.
Dokoki Kuma babu ruwan su da Mai Mulki ko talaka, a Musulunci kenan, a dokar Democracy ne ma zaka ji ance wai ba'a Kai shugaban kasa Kara, ba'a Kai Mataimakin sa, haka gwamna da Mataimakin sa, idan suna kan kujerar Mulki ba'a taba su, inji 1999 Constitution, Section 308.
~ Musulunci bai San da wannan ba.
So, Aminu yayi laifi, Aisha Buhari tayi laifi, amma mutanen mu da yawa sun fi a dinga magana ta Molon ka ne kawai, na cewa ai albarkacin bakin sa ya fada, ko a America babu freedom of speech anyhow.
~ Shugaba Idi Amin yana cewa 'yan kasar sa:
"You have a freedom of speech, but Freedom after speech that I cannot guarantee you".
~ Sa'annan su jami'an tsaron da suka kama Aminu a tuhume su, suna aiki da dokar kasa ne ko suna aiki da umarnin First lady, Kotu ce kawai zata bamu warranty of arrest kuje ku kama mutum ku kama shi.
~ Aminu zai iya shigar dasu Kara waye ya basu izinin su kama shi?
Laifin da ake zargin da aikatawa ba laifin da aka Halatta wa jami'an tsaro kama mutum bane ba tare da izinin Kotu ba.
~ Idan jami'an tsaro suka ganka kana harbi, ko kana fasa kayan gwamnati ya halatta su kama ka ko kotu bata basu izzini ba, Amma wannan is a civil case, ba crime bane balle Aisha tayi amfani da karfin mulkin mijin ta tasa a kama shi.
~ Kotu ita za tayi amfani da ikon ta wajen hukunta Aisha, Kuma Aminu yana da iko ya shigar da ita Kara akan tsare shi da aka yi har sama da 48 hours, zai iya neman Kotu ta tilasta Aisha ta biya shi wasu makudan kudade akan tsare shi da aka yi.
Ko Kuma yayi Karan jami'an tsaron da suka kama shi ba tare da izinin kamu (Warrant of arrest) daga Kotu ba.
Dan haka a hukunta Aminu yadda ya kamata, itama a hukunta ta yadda ya kamata, domin ta Sabawa kundin tsarin mulkin Nigeria.
~ Saboda kama Aminu ba tare da izinin Kotu ba, ba tare sahalewar Kotu kan tsare shi sama da 48 hours ba.
Abinda ya kamata ka sani shine laifi dai laifi ne ko Fir'auna kayi wa laifin ba za'a ce kayi dai dai ba, wannan shine abinda ya kamata kowa ya yarda dashi.
Muna magana akan doka ne fa ba yadda ake gudanar da Nigeria ba.
~ Dan kana jin haushin Buhari ko gwamnatin sa ba zai sa a ilmance ace abinda Aminu yayi dai dai ne ba, laifi dai laifi ne kawai, Koda dokar ba za tayi aiki akan kowa ba sai talaka still laifi ne, haka kuma duk sonka da gwamnatin Buhari ko kaunar ta Aisha tayi laifi ta Sabawa dokar kasa, don mijin ta ne yake Mulki ba za'a taba cewa itace akan gaskiya zalla ba.
✍️
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
No comments:
Post a Comment